Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), da ta tabbatarda shugaban ƙungiyar ƴan a-waren Biafra Nnamdi Kanu ya samu ‘cikakkiyar walwala’ yayin da yake tsare a hannunsu.
Umurnin ya biyo bayan ƙorafin da lauyoyinsa suka yi na cewa wanda suke karewa an hana shi walwala tareda hana shi canza kaya da yin addininsa a lokacin da yake tsare.
Sauraren shari’ar gaggawar da aka yi ya biyo bayan ƙorafin da lauyoyinsa suka yi cewa ɗage shari’ar da aka yi tun da farko ya saɓawa ka’da.
Kanu wanda ake tuhuma da cin amanar ƙasa bai halarci zaman kotun ba a ranar Alhamis din nan ba, inda aka ɗage shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2022.
Idan ba’a manta ba a kwanakin baya shugabannin ƙabilar Igbo sun roƙi shugaba Muhammadu Buhari da ya saki Nanmdi Kanu, buƙatar da shugaban ya ce ta yi nauyi sosai.

