Home Labaru Kotu Ta Ba EFCC Izinin Tsare Bello Adoke Tsawon Kwanaki 14

Kotu Ta Ba EFCC Izinin Tsare Bello Adoke Tsawon Kwanaki 14

415
0

Wata kotu da ke zama a Abuja, ta ba hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC damar tsare Mohammed Bello Adoke a hannun ta har na tsawon makonni biyu.

EFCC dai ta samu damar ne, bayan ta kama Adoke jim kadan bayan saukar sa a filin jirgin sama na Abuja, inda ‘yan sandan kasa-da-kasa su ka yo ma shi rakiya daga kasar Dubai.

Rahotanni sun ce lauyan Adoke ba ya cikin zauren kotun a lokacin da aka ba hukumar EFCC wannan dama, inda mai shari’a O.A. Musa ya bada umarnin a tsare Adoke na tsawon kwanaki 14 yayin da ake ci-gaba da bincike da kuma yi ma shi shari’a.

Mohammed Bello Adoke dai ya taba rike mukamin Ministan Shari’a kuma babbban lauyan Gwamnatin Tarayya a zamanin mulkin Goodluck Jonathan.

Tun a shekara ta 2017 EFCC ta fara tuhumar sa da kamfanonin mai na Malabu da Shell da Agip da wasu mutane da dama, bisa zargin almundahana a cinikin wata rijiyar man fetur.

Leave a Reply