Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kotu Ta Amince Da Korafin Atiku Kan Tinubu Dangane Da Jami’ar Chicago Da Shaidar NYSC

Kotun sauraren korafe-korafen zabe da ke Abuja, ta amince da shaidar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya gabatar.

Rahotanni sun ce, Kotun ta karbi takardun ne, wadanda su ka hada da takardar shaidar bautar kasa da ta kammala digiri da kuma takardar shaidar aiki a kamfanin Mai na Mobil da ke Nijeriya.

Jam’iyyar PDP ta gabatar da shaidar ne ta hannun Mike Enahoro Ebah, wanda ya ce ya karbi takardun Tinubu, amma su na dauke da sunan wani Bola Adekunle Tinubu.

Jagoran lauyoyin jam’iyyar PDP Chris Uche, ya ce mai bada shaidar ya kuma gabatar da wasu takardu da wasika zuwa ga hukumar zabe.

Sai dai Lauyan hukumar zabe Abubakar Mahmud da lauyan Tinubu Emmanuel Ukala da na jam’iyyar APC Lateef Fagbemi sun ki yarda da shaidun da jam’iyyar PDP ta gabatar.

Exit mobile version