Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kotu Ta Aika Wa Shugaban INEC Sammace

Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta kasa, INEC

Kotun sauraren kararrakin zaben Shugaban kasa, ta bada umurnin aika wa shugaban Hukumar zabe ta kasa Farfesa Mahmud Yakubu da kwamishinan zabe na jihar Zamfara takardar sammace.

Kamar yadda yak e kunshe a cikin takardar sammacen, ana sa ran  mutanen biyu za su gurfana gaban kotu su gabatar da wasu takardu da aka yi amfani da su a zaben da ya gabata, kamar yadda jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar su ka bukata.

Karanta Labaru Masu Alaka: Abin Da Jam’iyyu Suka Kashe A Zaben 2019

Yayin da aka fara zaman sauraren shari’ar, lauyan masu kara Chris Uche ya shaida wa kotun cewa, an aika wa mutanen takardar sammace, amma babu ko daya daga cikin su da ya gurfana ko kuma takardun da aka bukata.

Mai shari’a Mohammed Garba, ya ce bisa ga bayanan da kotu ta tattara, an ba Farfes Mahmud takardar sammacen shi ranar 15 ga watan Yuli na shekara ta 2019, lokacin da aka bukaci ya gabatar da takardun.

Exit mobile version