Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta aika wa Atoji Janar na tarayya da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC sammaci, cewa su gurfana a gaban ta a kan lamarin da ya shafi kayayyaki da dukiyoyin tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul-Aziz Yari.
An dai bukaci bangarorin biyu sun bayyana a kotun, domin su bada dalilin da ya sa ba za su janye matakin rufe asusun bankin Abdul-Aziz Yari ko kwace kadarorin sa har zuwa lokacin da za a saurari karar sa ba.
Mai shari’a Nkeonye Maha ya bada umurnin, bayan sauraren korafe-korafen da ke cikin karar daga bangaren lauyan Abdul-Aziz Yari, Mahmud Magaji.
Alkalin kotun, ya kuma bada umurnin a aika takardar sammacin a cikin sa’o’i 48, sannan a karshe ya dage zaman sauraren shari’ar zuwa ranar Alhamis mai zuwa.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/libertytvnews
Twitter: https://twitter.com/libertytvnews
Instagram: https://instagram.com/libertytvng
Liberty Radio 103.3 FM Abuja Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/libertyradioabuja
Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/tasharyancikaduna ?
Kira ??? +1-701-719-6971 don suraren (Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna) kai tsaye ta wayar hannu. Musamman Ga Waɗanda Suke Ƙasar Amurka.
Kuna iya turo mana labari ko shawara a: info@libertytvradio.com

