Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kotu A Najeriya Ta Umarci DSS Da Ta Baiwa Nnamdi Kanu Damar Ganin Likita

Mai shari’a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya da ke Abuja,
ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ba shugaban
masu rajin kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu damar ganin
likitan da ya ke so bisa bukatar a yi masa tiyatar kunne cikin
gaugawa sakamakon rashin lafiyar sa da aka ruwaito.

Da ta ke yanke hukuncin, Mai shari’a Nyako ta umurci ‘yan sandan na farin kaya su sa ido, tare da tattara bayanan da su ka danganci lafiyar Nnamdi Kanu domin dalilai na tsaro.

Alkalin kotun, ta kuma yi watsi da karar farko da hukumar DSS ta shigar ta na kalubalantar bukatar da ke gaban ta, wadda ke cewa Nnamdi Kanu ya na da hakkin duba lafiyar sa ko da a tsare.

Kotun, ta kuma bada umarnin a bada dukkan bayanan lafiyar Nnamdi Kanu ga shugaban kungiyar ta IPOB.

Exit mobile version