Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Korona A Najeriya: Mutum 10 Sun Mutu 397 Sun Kamu Ranar Litinin

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC t ace Ƙarin mutum 10 ne suka mutu sakamakon cutar korona a Najeriya a ranar Litinin.

Sabbin alƙaluman da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ya kuma nuna cewa ƙarin mutum 397 ne suka kamu da cutar a ranar ta Litinin.

Ta ce an samu sabbin wadanda suka kamu da cutar ne a jiha 18 har da babban birnin tarayya Abuja kuma sun haɗa da Legas (144) da Filato (83) da Kaduna (48) da Adamawa (36) da Rivers (22) da Oyo (16) da Kebbi (10).

Sauran jihohin su ne Nasarawa (7) da Sokoto (7) da Abuja (5) da Kano (5), da Edo (4),da Jigawa (3), da Ogun (2), da Akwa Ibom (2), da Neja (1), Bauchi (1), Zamfara (1).

Ya zuwa yanzu, jumillar mutum dubu 84 da 811 ne suka kamu da cutar a Najeriya, dubu 1 da 264 da cikin su sun mutu sannan dubu 71 da 357 sun warke.

Exit mobile version