Home Labaru Korafin Zabe: Lauyoyin Atiku Sun Ce INEC Ta Ki Bin Umarnin Kotu...

Korafin Zabe: Lauyoyin Atiku Sun Ce INEC Ta Ki Bin Umarnin Kotu Na Bada Kayan Zabe A Yi Bincike

266
0

Lauyoyin da ke kare Atiku Abubakar da Peter Obi a kotun sauraron karar zabe, sun koka da yadda hukumar zabe ta ki bada kayan da aka yi amfani da su a zaben da ya gabata domin su duba.

Idan dai ba a manta ba, kotun daukaka kara ta ba hukumar zabe umurnin ta ba lauyoyin Atiku kayan da aka yi amfani da su a zaben domin yin bincike a kan su, amma har yanzu hukumar ta ki bin wannan umarni.

Daya daga cikin manyan Lauyoyin da ke kare Atiku Abubakar da Peter Obi Silas Onu ya shaida wa manema labarai cewa, an hana su ganin dukkan kayayyakin  da aka yi zabe da su duk da cewa sun cika sharuda tare da biyan kudin aiki.

Ya ce ganawa da masu kare hukumar zabe a gaban kotun ya na neman ya zame masu wahala, amma ya sha alwashin ci-gaba da kokarin ganin hukumar ta bi umarnin da aka ba ta na ba su kayan da aka yi aiki da su a zaben shekara ta 2019.

Silas Onu, ya ce idan lamarin ya ci tura, za su nemi su maka shugaban hukumar zabe farfesa Mahmud Yakubu da sauran manyan jami’an hukumar a gaban kotu, bisa laifin bijire wa umarnin babbar kotu.