Wata babbar kotu tarayya da ke Abuja, ta soke nasarar da zababben sabon dan majalisar wakilai na mazabar Zaki ta jihar Bauchi a karkashin jam’iyyar APC Omar Tata ya samu.
Alkalin kotun mai sharia Bello Kawu ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu, inda ya haramta sanar da sunan Tata a matsayin wanda ya lashe zaben.
Mai shari’a Bello Kawo, ya umarci hukumar zabe ta mika wa abokin hamayyar sa na jam’iyyar PDP Jatau Muhammad Auwal shahadar samun nasara, wanda shi ne yazo na biyu a zaben.
A cewar kotun, jam’iyyar APC ba ta da dan takara, kuma babu yadda za a yi ta tsaida dan takara a zaben kujerar dan majalisar wakilai, domin dan takarar jam’iyyar PDP ya ce Omar Tata bai cancanci tsayawa takara ba, saboda APC ba ta gudanar da zaben fidda gwani wajen tsaida shi takara ba.
Bayan kotun ta gamsu da bayananan Jatau, ta bayyana kuri’un da Tata ya samu a matsayin haramtattu, da haka Jatau na jam’iyyar PDP ya zama sabon dan majalisa.