Majalisar dattawa ta gayyaci ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola, kan yin watsi da aikin hanyoyin Mararraba da Mubi da Michika da Bama duk da biyan dan kwangilar sama da naira billiyan daya da rabi.
Dan majalisar dattawa Elisha Ishaku ya gabatar da koken a zaman majalisar, inda ya ce tun lokacin da aka fara aikin babu wani ci gaba da ka samu.
Majalisar ta umurci kwamitin ayyuka ya binciki matsayar da aka cimmawa a aikin da kuma dalilan da suka sa aka yi watsi da aikin duk da cewa an biya kudin aikin.
Shugaban majalisar ya bukaci kwamitin ya gayyaci ministan ayyuka da gidaje domin jin makasudin watsi da ayyukan, sannan ya gabatar da rahoton sa a cikin makwanni 2 masu zuwa.
Dan majalisa Ishaku, ya ce rashin
kyan hanyar da kuma dakatar da aikin ya haifar da wahalhalu rayuwa ga mutanen
yankin da kuma koma bayan tattalin arzikin.