Home Labaru Korafi: Kotun Zaben Shugaban Kasa Ta Fara Zaman Ta Na Farko

Korafi: Kotun Zaben Shugaban Kasa Ta Fara Zaman Ta Na Farko

276
0

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP Peter Obi, da manyan ‘yan siyasa da lauyoyin jam’iyyun PDP da APC sun halarci kotun sauraren kararrakin zaben Shugaban kasa da aka fara.

Shugabar kotun daukaka kara mai shari’a Zainab Bulkachuwa da ta jagoranci zaman farko, ta yi alkawarin cewa za su bi doka wajen gudanar da shari’ar da ke gaban su.

Ana sa ran kotun za ta fara sauraren karan da Atiku Abubakar ya shigar a kan jam’iyyar APC da dan takarar ta Shugaba Muhammadu Buhari.

Daga cikin mahalarta zaman kotun kuwa akwai lauyoyin mai kara Atiku Abubakar da jam’iyyar sa PDP, da lauyoyin Shugaba Buhari da jam’iyyar APC da kuma lauyoyin hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa.

Jam’iyyar PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar ne su ka shigar da karar, inda su ke kalubalantar sakamakon da hukumar zabe ta kaddamar da Shugaban kasa.

Leave a Reply