Home Labaru Korafi: Gwamna Ortom Ya Ba Masu Zanga-Zanga Hakuri A Kan Rashin Biyan...

Korafi: Gwamna Ortom Ya Ba Masu Zanga-Zanga Hakuri A Kan Rashin Biyan Su Hakkokin Su

329
0

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya ba masu zanga-zanga hakuri sakamakon gazawar gwamnati na biyan su hakkokin su.

Samuel Ortom ya bada hakurin ne a lokacin da ya ke yi wa fusatattun ma’aikatan jawabi ne a kofar shiga gidan gwamnatin jihar a ranar juma’ar da ta gabata.

Gwamna Ortom ya ce, sun gaji matsalar ne tun daga gwamnatin da ta gabata, amma ya yi alkawarin shawo kan matsalar nan da wani lokaci mai zuwa.

Ya ce wasu sun samu kudin su kwanaki biyu da suka gabata, kuma an kara amincewa a bada naira miliyan 611 domin biyan masu tsaffin ma’aikata hakkokin su watan Afirilu da Mayu.

A jawabin shugaban tsaffin ma’aikatan Peter Kyado ya hori gwamnatin jihar da ta cika alkawarin da ta yi masu domin kawo karshen zanga-zangar.

Leave a Reply