Hamshakin attajiri, kuma dattijon Arewa, Alhaji Aminu Ɗantata ya ce yanzu duniya yana binta ne sannu a hankali amma ba daɗinta ya ke ji ba.
Alhaji Aminu Ɗantata dake da shekaru 91 a duniya ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi, bayan ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC Kashim Shettima ya kai masa ziyara a gidan sa dake Unguwar Koki dake birnin Kano.
Aminu Ɗantata, wanda shi ne kawun Aliko Dangote ya ce ba bu sauran abin da ya rage masa yanzun lokaci kawai ya ke jira domin da yana da abokai a faɗin jihohin Najeriya, amma yanzu babu mutum 10 da suka rage suna raye.
Attajirin ya ce tsakanin sa da Allah baya jin daɗin duniyar nan yanzu, komawar sa ga ALLAH kawai ya ke jira, fatar sa shine Allah ya sa mu gama da duniya lafiya.
Ya ce yana rokon duk wanda ya yi wa laifi ya yafe masa shi ma ya yafewa duk waɗanda suka yi masa laifi, ya ce yanzu shi kaɗai ya rage cikin ƴan uwan sa sai tarin jikoki aka bar masa.
Alhaji Aminu Ɗantata mashahurin attajiri ne mazaunin garin Kano wanda ya gaji arziki, mahaifin sa Alhassan Ɗantata, ya taba zama wanda ya fi kowa tarin dukiya a yankin Afrika saboda fice da yayi a harkar kasuwanci.

