Home Home Ko Ni Na Tambaye Ka Fuloti A Abuja, Kada Ka Ba Ni...

Ko Ni Na Tambaye Ka Fuloti A Abuja, Kada Ka Ba Ni – Tinubu Ya Faɗa Wa Wike

40
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci ministan Birnin Tarayya Nyesom Wike da cewa, kada ya ba shi fili kyauta ko da ya nemi hakan.

Tinubu ya bayyana haka ne, a wajen taron kungiyar lauyoyin Nijeriya NBA da ya gudana a Abuja, inda ya ja hankalin Wike ya bayar da fifiko wajen kammala aikin hanyoyin cikin birnin Abuja domin ci-gaban al’umma.

Shugaba Tinubu ya ce manufar sa ba wai ya samu filaye kyauta ba ne, amma ya tabbatar da an samar da jirgin ƙasan da zai riƙa jigilar al’umma a cikin birnin.

Nysom Wike dai ya riƙa haifar da muhawara tun bayan zama minista, sakamakon alwashin da ya ci na rusa gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.

Yayin wata ziyarar gani da ido, Ministan ya ce ya kamata a kammala aikin layin jiragen kasa na birnin Abuja nan da watanni takwas masu zuwa.