Wani binciken baya-bayan nan ya tabbatar da cewa, abincin da ake sayarwa a bude a kan titunan Lagos da Kano ya na dauke da cututtuka.
Binciken ya ja kunnen mazauna manyan biranen biyu da su yi kaffa-kaffa daga sayen abincin da ba a cikin gidajen su aka dafa ba, musamman wanda ake sayarwa a gefen tituna.
Rahoton ya kuma nuna cewa, abincin cike ya ke da gurbatattun sinadarai da magungunan kashe kwari da tarkacen kananan karafuna da sauran su. An kuma bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta hana talla da saida abinci barkatai a kan tituna, domin zai rage illar cin gurbataccen abinci mai barazana ga lafiyar jama’a da dama.