Home Labaru Kishin Kasa: Za Mu Ba ‘Yan Jam’iyyun Adawa Mukamai A Majalisa –...

Kishin Kasa: Za Mu Ba ‘Yan Jam’iyyun Adawa Mukamai A Majalisa – Gbajabiamila

328
0
Tilas Nijeriya Ta Cigaba Da Kasancewa Kasa Daya Dunkulalliya – Gbajabiamila
Tilas Nijeriya Ta Cigaba Da Kasancewa Kasa Daya Dunkulalliya – Gbajabiamila

Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya ce majalisar ba za ta maida ‘yan jam’iyyun adawa saniyar ware wajen nadin mukamai na jagorancin wasu kwamitoci ba.

Femi Gbajabiamila, ya ce zai kawo sauyin tsare-tsare a majalisar domin inganta ci-gaba sabanin yadda ta kasance a baya.

Furucin Gbajabiamila dai ya zo ne yayin amsa tambayoyin manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja, jim kadan bayan ganawar sa da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Sai dai manufar Gbajabiamila ta ba ‘yan jam’iyyun adawa damar jagorantar kwamitoci a majalisar ta ci karo da kudirin shugaban jami’yyar APC na kasa.

Idan dai za a iya tunawa, yayin wata liyafa da shugaba Buhari ya shirya wa zababbun ‘yan majalisar Tarayya, Oshiomole ya ce ‘yan jami’yyun adawa ba za su samu damar numfasawa ba a wannan karon wajen rike mukamai, sabanin kuskuren da jam’iyyar APC ta tafka a shekara ta 2015.

Leave a Reply