Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jinjina wa daukacin al’ummomin Nijeriya da su ka kaurace wa kiraye-kirayen da aka rika yi a shafukan sada zumun ta, cewa su fito zanga-zangar juyin-juya hali, inda su ka maida hankali ga harkokin gaban su.
Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Ya ce shugaba Buhari ya ji dadin goyon bayan da aka ba tafiyar dimokradiyya a Nijeriya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce, duk da akwai daruruwan mutanen da su ka shiga gangamin, sun yi hakan ne domin cimma muradun kawukan su ba da nufin ci-gaban kasa ba.