Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, tare da sarkin Maradun Alhaji Garba Tambari a wata liyafar shan ruwa da ta gudana a kasar Saudiyya.
Babban mai Magana da yawun shugaban kasa malam Garba Shehu, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
A jawabin a lokacin shan ruwan, shugaba Buhari ya nuna damuwar sa a kan kashe rayukan mutane barnatar da dukiya sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a jihar Zamfara.
Garba Shehu ya ce, shugaba Buhari ya tabbatar da cewa za su yi adalci domin ganin dukkanin ‘yan Nijeriya sun samu kwanciyar hankali da cigaba a duk inda suka samu kan su.
Sarkin Muradun shi ya jagoranci addu’o’i ga wadanda suka rasa rayukan su sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda a jihar Zamfara da ma fadin Nijeriya, sannan ya yi addu’ar Allah ya ba Nijeriya zama lafiya da karuwar ar’ziki.