Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika da tawaga ta musamman zuwa Sokoto da Katsina sakamakon yadda ƴan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a yankunan jihohin.
Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya sanar da hakan inda ya ce shugaba Buhari, yana jiran rahoto cikin gaggawa da kuma shawarwari kan matakin da ya kamata a ɗauka domin magance matsalolin da jihohin ke fuskanta.
Cikin waɗanda Shugaban kasan ya tura, akwai babban mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, da Babban Sufeton ƴan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya Yusuf Magaji Bichi, da kuma shugaban tsaro na rundunar sojin Najeriya Manjo Janar Samuel Adebayo.
You must log in to post a comment.