Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon faifen bidiyo da take bayyana cewa ita ke da alhakin kai hari tare da hallaka manoman shinkafa fiye da 40 a kauyen Kosheba da ke Zabarmari a jihar Borno.
Boko Haram ta ce ta hallaka manoman ne saboda sun kama wasu dakarun ta sun mika su a hannun sojin Najeriya da ke gudanar da aiki a yankin.
Da ma dai tun bayan da aka kai harin mutane da dama suka fara zargin cewa mayakan na Boko Haram ne suka aikata mummunar aika-aikar, wanda baya rasa nasaba da yadda ‘yan kungiyar suka dade suna kai irin wadannan hare-hare a yankunan daban-daban na jihar Bornon.
A ranar Asabar din da ta gabata ne maharan suka kai farmaki cikin gonakin a yankin Koshebe na kauyen Zabarmari da ke karamar hukumar mafa a jihar Borno inda suka kashe fiye da mutum 40 ta hanyar yi musu yankan rago.