Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kisan Kai: Kotu Ta Yi Wa Wanda Ya Kashe Marasa Lafiya 85 Daurin Rai-Da-Rai A Jamus

Kotu ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga Niels Hoegel, wani dan kasar Jamus da aka kama da laifin kashe masara lafiya 85 a lokacin da ya ke aiki a matsayin mai kula da marasa lafiya.

A ranar Alhamis da ta gabata ne aka yanke masa hukuncin, bayan shi da kan sa ya amsa laifin rika yi wa marasa lafiya allurar kisa a wani asibitin kasar Jamus.

Asirin Hoegel dan shekara 42 dai ya fara tonuwa ne, bayan an same shi da laifin kashe wasu marasa lafiya biyu a shekara ta 2015.

An gano cewa, Hoegel ya rika yi wa jama’a allurar dakatar da bugawar zuciya a asibitocin Oldenburg da Delmenhorst a kasar Jamus daga shekara ta 2000 zuwa 2005.

Masu gabatar da kara sun ce, Hoegel ya rika yin haka ne da nufin idan marar lafiya ya suma, sai ya farfado da shi domin wai ya burge likitoci ‘yan’uwan sa tare da nuna masu kwarewar sa.

Da farko dai takardar zargin da aka yi masa ta nuna cewa ya kashe marasa lafiya 100, amma ya yi gardama da cewa mutane 43 kawai ya san ya kashe.

Exit mobile version