Home Labaru Kisan Funke: Za A Tsaurara Matakan Tsaro A Kudancin Nijeriya – Sufeto...

Kisan Funke: Za A Tsaurara Matakan Tsaro A Kudancin Nijeriya – Sufeto Janar

293
0
Mohammed Adamu, Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya bada umarnin kawo sabbin tsare-tsare a kan manyan hanyoyin kudancin Nijeriya.

Mohammed Adamu, ya ce rundunar ta yi nisa wajen shirye-shiryen kafa shirin ‘Operation Puff Adder, wanda shiri ne da ake amfani da shi a arewacin Nijeriya domin yaki da masu satar shanu da masu garkuwa da mutane da ke sace jama’a kan hanya musamman daga Kaduna zuwa Abuja.

An dai dauki wannan mataki ne bayan wasu ‘yan bindiga sun harbe Funke Olakunrin, wadda ‘ya ce ga shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere Chif Reuben Fasoranti.

Chif Fasoranti

Shugaban ‘yan sandan, ya ce wannan yunkuri ne na dakile makamancin wannan mummunan lamari da ya faru da Funke Olakunrin, ya na mai yi wa shugaban kungiyar Afenifere alkawarin cewa za a yi bincike domin gano masu hannu a kisan domin hukunta su. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Nijeriya Frank Mba ya fitar, ta ce tuni rundunar ta tura jami’an tattara bayanan sirri domin nemo masu hannu a kisan.