Nijeriya ta janye jakadan ta na kasar Afrika ta Kudu Ambasada Kabiru Bala, tare da kaurace wa taron tattalin arziki na duniya da aka fara a ranar Larabar nan a birnin Cape Town na kasar Afirka Ta Kudu.
Wata majiya daga fadar Shugaban kasa ta bayyana wa manema labarai cewa, Nijeriya ta kuma bukaci a biya ta diyya akan rayukan ‘yan Nijeriya da dukiyoyin su da su ka hallaka a harin Afrika ta Kudu.
A cewar majiyar, hakan ya biyo bayan ganawar da ta gudana tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da Osinbajo da ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama, dangane da hare-haren da ake kaddamarwa a kan ‘yan Nijeriya a kasar Afrika ta Kudu.
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya kamata ya wakilci Nijeriya a wajen taron, wanda za a yi na tsawon kwanaki uku.