A ranar Juma’a ne gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatin jihar zata kashe Naira miliyan 318 wajen gina filin atisaye na sojoji a dajin Falgore inda yanzu yan ta’adda ke fakewa.
Ganduje, ya bayyana hakan ne alokacin rufe bikin gasar sojojin bataliya ta daya da aka gudanar a barikin sojoji ta Bakuvu dake Kano. Yace idan sojoji na a dajin to yan ta’adda da masu gakuwa da mutane da sauran kungiyoyin yan ta’adda zasu ji tsoro su bar wajen.
Gwamnan yace Za a dora tushen ginin wannan muhimmin aiki kwanannan kuma zai zama gagarumar nasara wajen magance matsalolin tsaro a jihar.
Gwamnan ya kara da cewa gasar da sojojin suka gudanar ya kara tabbar da kokarin sojoji na ganin cewa sun magance matsalolin tsaro a kasar nan.
Tun farko, babban sojin bataliyar, Maj-Gen Faruk Yusuf, ya ce gasar na da zummar karawa sojoji sanin dabarun yaki, hadin kai, da kuma shugabanci da dai sauran su.