Kenya tana fuskantar yiwuwar Fifa ta haramta mata shiga gasa bayan Ministar Wasannin kasar ta bayar da umarni ga kwamitin rikon kwarya ya gudanar da harkokin wasannin kasar.
Ministar Wasannin kasar Amina Mohamed ta kafa kwamitin rikon kwarya ne mai kunshe da mutum 27 domin tafiyar da Hukumar kwallon Kafar Kenya.
Fifa ba ta yarda wata gwamnati ta tsoma baki wajen gudanar da hukumar kwallon kafa ta wata kasa ba kuma a baya ta haramta wa kasashen da suka yi irin wannan katsalandan shiga duk wasu harkokin kwallon kafa.
Ministar wasannin ta ce a kokarin su na kare martabar kwallon kafa, ne suka yanke shawarar kafa kwamitin rikon kwarya na hukumar kwallon kafa wanda zai yi wata shida yana aiki.