Iyalan jami’an tsaron da aka kashe a jihar Kebbi sun gudanar da zanga zanga.
Mahukuntan jihar Kebbi dai sun bukaci a gudanar da addu’o’in neman jin-kai ga jami’an da sauran wadanda su ka rasa rayukan su sanadiyyar ayyukan ta’addanci.
Jami’an soji da ‘yan sanda goma sha tara ne ‘yan bindiga suka kashe a garin Kanya dake yankin masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi.
Tun daga ranar da ‘yan bindiga su ka hallaka jami’an tsaro a wani harin kwanton-bauna da aka yi wa mataimakin gwamnan jihar bayan an kashe ‘yan sa-kai sama da 60, hankula sun karkata a jihar kebbi, inda jama’a ke ta jajenta wa gwamnati da iyalan wadanda su ka rasa rayukan su.
Sai dai wannan bai hana iyalan jami’an tsaron da aka kashe shiga damuwa da juyayi ba, inda har wasu rahotanni ke nuna sun fusata sun kuma gudanar da zanga zanga, inda wani bidiyo ya nuna su dauke da kwalaye har da cinna wa tayoyi wuta domin nuna damuwa.