Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kawar Da Yunwa: Gwamnati Ta Kashe Naira Biliyan 1.8 A Cikin Shekaru Biyu

Chris Isokpunwu, Shugaban Sashen Shirin Kawar Da Yunwa Na Ma’aikatar Lafiya

Chris Isokpunwu, Shugaban Sashen Shirin Kawar Da Yunwa Na Ma’aikatar Lafiya

Gwamnatin tarayya ta kashe akalla Naira biliyan 1 da miliyan 800 domin ciyar da kananan yara da ke fama da matsananciyar yunwa a jihohi 18 tsakanin shekara ta 2017 da 2018

Shugaban sashen shirin kawar da yunwa na ma’aikatar lafiya Chris Isokpunwu ya sanar da haka, a wata zantawa da ya yi da manema labarai a Abuja.

Isokpunwu, ya ce sakamakon binciken da ma’aikatar lafiya ta gudanar a shekara ta 2017, ya nuna cewa jihohi 18 a kasar nan su na fama da matsananciyar yunwa.

Ya ce a dalilin haka, gwamnati ta tsara matakai tare da hada hannu da Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya, domin ganin ta kawo karshen wannan matsala a Nijeriya.

Isokpunwu ya kara da cewa, a shekara ta 2017, gwamnati ta ware Naira biliyan 1 da miliyan 800, domin samar da kula ga kananan yaran da ke fama da matsananciyar yunwa a jihohin Anambara da Bayelsa da Edo da Bauchi da birnin tarayya Abuja.

Exit mobile version