Home Coronavirus Kaucewa Kamuwa Da Cutar Covid-19 Ta Sa Aka Hana Wasu Gwamnoni Tashi-...

Kaucewa Kamuwa Da Cutar Covid-19 Ta Sa Aka Hana Wasu Gwamnoni Tashi- Sirika

425
0
Kaucewa Kamuwa Da Cutar Covid-19 Ta Sa Aka Hana Wasu Gwamnoni Tashi- Sirika
Kaucewa Kamuwa Da Cutar Covid-19 Ta Sa Aka Hana Wasu Gwamnoni Tashi- Sirika

Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya ce an hana wasu gwamnoni biyar barin Nijeriya ne saboda gudun kamuwa da cutar Coronavirus.

Hadi Sirika ya bayyana haka ne a lokacin taron kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin yaki da annobar Coronavirus, wanda ya gudana Abuja, inda ya kara da cewa biyu daga cikin gwamnoni da aka hana jirgin tashi sun fito ne daga yankin kudu maso kudancin Nijeriya.

Ministan ya kuma tabbatar da cewa, akwai daya daga cikin gwamnonin da ya fito daga yakin watau Arewa ta tsakiya, yayin da sauran suka fito daga shiyyar kudu maso gabas.

Hadi Sirika ya cigaba da cewa, duk wani jirgi da zai bar Nijeriya zuwa wata kasa, sai bisa dole kuma kasha 98 cikin 100 na tafiyar za ta kasance ta na da alaka  da annobar Coronavirus.

Haka kuma minsnta ya ce, dai-dai-kun jirage da za su tashi suma za su kasance su na da huldar kasa da kasa, ko kuma masu daukar mutanen kasashen waje, wanda takardun su ke bi ta hannun ma’aikatar kasashen wajen  ta Nijeriya.