Wutar lantarki da aka ɗauke a zauren majalisar dokoki ta kawo
jinkirin fara zaman ƴan majalisar dattijai.
Sanatocin sun tsaya na wani lokici yayin da suke jiran kamfanin arraba lantarki na Abuja ya dawo da wutar.
Zauren Majlisar ya kasance cikin duhu yayin da wasu tsiraru daga cikin ƴan majalisar suke zaune suna jiran a dawo da wutar, amma daga baya shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya buɗe zaman bayan dawowar lantarkin.
Dama dai kamfanin lantarki ya koka kan cewa akwai ma’aikatu da hukumomin gwamnati da dama waɗanda yake bi bashi, har ma ya yi barazanar yanke musu lantarki matuƙar ba su biya bashin da ake bin su ba.
Najeriya dai na fama da ƙarancin wutar lantarki, inda ƙasar ta gaza samar da isasshen wutar lantarki da zai wadaci al’umma da masana’antu