Home Labaru Kasuwar ‘Yan Kwallon Kafa: Makomar Rice, Origi, Rojo, Ibanez, Haaland

Kasuwar ‘Yan Kwallon Kafa: Makomar Rice, Origi, Rojo, Ibanez, Haaland

321
0

Manchester United tana iya yunkurin daukar dan wasan West
Ham Declan Rice, ko da yake ana tunani dan wasan na Ingila
mai shekara 21 ya fi son tafiya Chelsea idan ya bar Hammers.

Wolves na sanya ido kan dan wasan Liverpool da Belgium
Divock Origi, mai shekara 25, wanda za a iya bari ya kama
gaban sa a watan Janairu.

Manchester United na kokarin ganin ta bayar da aron Marcos
Rojo a watan Janairu, a yayin da Newcastle ke son daukar dan
wasan na kasar Argentina, mai shekara 30.

Liverpool ta sanya dan wasan Roma Roger Ibanez a jerin ‘yan
wasan da take son dauka domin maye gurbin dan wasanta da ke
jinya dan kasar Netherlands Virgil van Dijk, mai shekara 29,
kuma za ta iya kashe £30m don dauko dan kasar ta Brazil.