Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya sanya wa
Kayode Egbetokun lambar ƙarin girma a matsayin sabon
shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya na na riko.
Kashim Shettima ya sanya lambar Karin girman ne lokacin wani taƙaitaccen biki a ofishin sa da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja.
Daga cikin muƙaman da ya riƙe a baya dai, sabon shugaban ‘yan sandan na riƙo ya taba riƙe mukamin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas.
Sauran jami’an da suka halarci taron akwai gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, da mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Nuhu Ribadu, da shugaban ‘yan sandan Nijeriya mai barin gado Usman Alkali Baba.