Home Labaru Kasar Guinea: Najeriya Ta Yi Allah Wadai Da Juyin Mulki

Kasar Guinea: Najeriya Ta Yi Allah Wadai Da Juyin Mulki

152
0

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga sojojin kasar Guinea da suka yi ikirarin kifar da gwamnatin Shugaba Alpha Conde da su yi maza su janye matakin da suka dauka.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasa ta fitar dauke da sa hannun mai magana da yawunta Esther Sunsuwa, ta ce, juyin mulkin da dakarun kasar suka yi, ya sabawa tsarin dimokradiyya da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO take karewa.

Gwamnatin tarayya na bakin cikin wannan juyin mulki da aka yi a Jamhuriyyar Guinea a ranar Lahadi, matakin da ya sabawa tsarin dimokradiyya da kungiyar ECOWAS take mutuntawa.

Gwamnatin ta yi Allah wadai da wannan juyin mulkin da kakkausan harshe, tana kuma kira ga wadanda ke da hannu a wannan lamari, da su mayar da kasar mai bin kundin tsarin mulkin ba tare da bata lokaci ba, su kuma kare rayuka da dukiyoyi.”

A ranar Lahadi ne wasu sojojin kasar suka yi ikirarin kifar da gwamnatin Conde a wani jawabi da suka yi ta kafar talabijin, amma sojojin sun yi ikirarin cewa gwammatin Conde na tafiyar da al’amuran kasar ta hanyoyin da ba su dace ba.