Home Labarai Kasafin Kudi: Tinubu Ya Sake Neman Tsawaita Wa’adi

Kasafin Kudi: Tinubu Ya Sake Neman Tsawaita Wa’adi

51
0
Tinubu (1)
Tinubu (1)

Tinubu ya bukaci Majalisa ta kara tsawaita wa’adin aiwatar da bangaren manyan ayyuka na kasafin na 2023,

da Naira tiriliyan 2 da biliyan 170 na karamin kasafin kudi daga ranar 30 ga watan yunin da muke ciki zuwa 31 ga watan disamba mai zuwa.

A watan Disambar bara ne, dukkanin zaurukan majalisar guda 2 suka tsawaita wa’adin aiwatar da bangaren manyan ayyuka

na kasafin kudin na shekarar data soma daga ranar 31 ga watan Disambar zuwa ranar 31 ga watan Maris din 2023.

Har ila yau, Shugaban Kasa ya kara neman karin wa’adin aiwatar da kasafin daga 31 ga watan Maris daya gabata zuwa 30 ga watan Yunin.

Sai dai Akpabio, ya ce babban kwamitin majalisar zai tattauna akan bukatar, bayan dawowa daga wani zaman sirri.

Haka kuma, Majalisar Dattawan tayi shiru na minti guda domin girmama marigayi Mataimakin Shugaban Hukumar Kwastam, Etop Essien,

wanda ya mutu a Talatar data gabata a cikin ginin majalisar tarayyar, yayin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan kwamitin majalisar akan asusun ajiyar gwamnati.

Leave a Reply