Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, ya ce daga yanzu majalisun dokoki za su rika tabbatar da cewa sun amince da kasafin kudi a cikin watanni 3 idan bangaren zartaswa sun gabatar.
Lawan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan kammala Sallar Juma’a a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Sannan ya ce majalisar na kyautata zato bangaren zartaswa ma za su rika yin dukkanin mai yiwuwa dan ganin sun gabatar da kasafin kudin da wuri dan ganin majalisar ta yi abin da ya kamata akan lokaci.
Ya ce akwai bukatar bangaren majalisar da kuma zartaswa su yi aiki tare musamman wajen kare kasafin dan ganin an gudanar da abubuwan da suka kamata akan lokaci.
Ya ce a so samun majalisa ne duk wani minister ko shugaban wata ma’aikata ko hukuma ya bayyana a gaban ta domin kare kasafin ma’aikatarsa kafin yin tafiya zuwa wata kasa.
Lawan ya ce za a bar kofa a bude na tsawon wata guda ga ministoci da shugabannin ma’aikatun su kare kasafin da aka gabatar musu.