Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci dukkanin ministocin sa da shugabanin hukumomin gwamnati su soke duk wata tafiya zuwa kasashen ketare har sai lokacin da aka kammala aikin kasafin kudin shekara ta 2020.
Direktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Wille Bassey ya sanar da haka a ranar juma’ar da ta gabata.
Sanawar ta kara da cewa, shugaban kasa Buhari ya kuma bada umurnin dakatar da duk wasu tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da ministocin sa ko shugabanin hukumomi za su yi, wanda hakan zai ba ministocin damar kare kasafin kudin da ke gaban majalisar dattawa.
Sannan
dakatar da tafiye-tafiyen zai ba hukumomi da ma’aikatun gwamnati damar bai wa
sashin masu zartarwa hadin kai da ya kamata, domin tabbatar da cewa an amince
da kasafin kudin a kan lokaci.