Home Labaru Kasafin 2019: Shugaban Kasa Zai Kashe Naira Biliyan 1 A Kan Tafiye-Tafiye

Kasafin 2019: Shugaban Kasa Zai Kashe Naira Biliyan 1 A Kan Tafiye-Tafiye

394
0

Bayanan kasafin shekara ta 2019 sun nuna cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kashe kimanin naira biliyan daya a tafiye-tafiyen gida da waje.

Kamar yadda yake kunshe a cikin kasafin, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai kashe naira miliyan 217 da dubu 60 a tafiye tafiyen ketare, yayin da zai kashe naira miliyan 83 da 74,000 a kan tafiye-tafiyen gida.

Haka kuma, an ware naira biliyan 3 da miliyan 822 domin kula da kayan wuta da duk wata na’ura a fadar shugaban kasa.

Bayanan kasafin sun cigaba da cewa, an ware naira miliyan 576 da dubu 747 domin canza motoci da kayayyakin su, da tayoyin motocin tawagar tsaro da kuma motocin ayyuka a fadar shugaban kasa.

Haka kuma, Shugaban kasa zai kashe naira miliyan 164 da dubu 176 a kan ayyukan kwararru da alawus na zama, da kuma naira miliyan 25 da dubu 652 a kan kayan abinci da kiwon liyafa.

Leave a Reply