Shugaban hukumar Alhazai a Najeriya, Alhaji Jalal Ahmad Arabi ya ce akwai yiwuwar hukumar ka iya mayar wa maniyyata rarar kuɗin da suka biya sakamakon karyewar farashin dalar Amurka.
Alhaji Jalal Arabi ya shaida hakan ne a wata hira da manema labarai wadda kuma hukumar alhazan ta wallafa a shafinta na X, ranar Alhamis.
Ya ƙara da cewa indai da rai da lafiya kuma idan dai su ne a kan kujerar to ba za su zauna a kan haƙƙin kowa ba da izinin Allah. za su tabbatar sun biya wannan rarar.
To sai dai shugaban hukumar ta Alhazan na Najeriya bai faɗi lokacin da za a mayar wa maniyyatan rarar kuɗaɗen nasu ba.
A mafi yawancin lokuta dai hukumar ta Alhazai kan mayar wa alhazai rarar kudaɗen ne bayan kammala aikin Hajji.
A yanzu haka dai naira na ci gaba da samun tagomashi a kan dalar Amurka inda bayanai ke nuna farashin dala a kasuwar bayan fage na tsakanin naira dubu ɗaya da ƙasa da haka.