Home Labaru Kasuwanci Karuwar Darajar Naira: Shugaban Ƴan Canji Ya Ce Suna Sayen Dala Daga...

Karuwar Darajar Naira: Shugaban Ƴan Canji Ya Ce Suna Sayen Dala Daga Gwamnati Kan Naira 980

49
0
Alhaji Aminu Gwadabe 1062x598
Alhaji Aminu Gwadabe 1062x598

Ƙungiyar ƴan canji ta Najeriya ta ce ƴan canji sun fara sayan dala ɗaya a kan naira 980 a kasuwar bayan fage sannan su sayar kan naira 1,020.

Shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Aminu Gwadabe ne ya tabbatar da haka a hirar sa da manema labarai inda ya ambaci cewa darajar naira ta ƙaru a lokaci kaɗan da ba a taɓa tsammani ba.

Gwadabe ya jinjinawa gwamnati da kuma babban bankin ƙasa kan ƙoƙarin su inda ya ce wannan ne karon farko cikin shekara 15 da farashin dala a kasuwar ƴan chanji ke ƙasa da farashin da ake saidawa a hukumance.

Ya shaida cewa yanzu babu raɗe-raɗin da ake yawan yi da ke zuzuta farashin dala.

Gwadabe ya ƙara da cewa a halin yanzu suna siya daga gwamnati a kan naira 980 sannan su sayar a kan naira 1,020.

Leave a Reply