Home Labaru Karshen Alewa: Dubun Mai Damfara Da Sunan Ahmed Musa Ta Cika

Karshen Alewa: Dubun Mai Damfara Da Sunan Ahmed Musa Ta Cika

252
0

’Yan sandan a Jihar Kano sun kama wani matashi da ke damfarar mutane a jihar da sunan kyaftin na babban kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Ahmad Musa.

Mai Magana da yawun ’yan sandan Jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama matashin ne bisa laifin damfarar mutane.

Ya ce bayan an yi wa kwamishinan ’yan sandan jihar CP Habu Sani korafi, nan take ya ba da umarnin cafko wanda ake zargin kuma ya amsa laifin nasa nan take.

Da aka bincike shi ya ce ya damfari mutum sama da 15 da ya sayar musu da takarda a kan kudi naira dubu 5, kuma ya hada kudi sama da naira dubu 700, inda ya kashe wa ’yan matan sa a wani Otal dake unguwar Sabon Gari.

Musa Muhammad daga Unguwar Hotoro a Kano ne ya shigar da korafi a kan wanda ake zargin, wanda tsohon ma’aikacin wajen motsa jiki ne mallakar Ahmed Musa.

Wanda ake zargin ya amsa cewar yana damfarar matasa ne dake son tafiya kasashen ketare buga kwallon kafa da sunan dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles.