Home Labaru Kariya: FRSC Ta Bukaci A Ba Jami’an Ta Damar Rike Makamai

Kariya: FRSC Ta Bukaci A Ba Jami’an Ta Damar Rike Makamai

299
0

Shugaban majalisar amintattu na hukumar kiyaye hadurra ta kasa Mallam Buhari Bello, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sama wa ma’aikatan ta makaman za su taimaka wajen gudanar da ayyukan su da kuma kare kan su.

Buhari Bello ya bayyana haka ne, a wajen bikin kaddamar da sabbin motocin sintiri guda 77 da ya gudana a Abuja, inda ya ce ta’addanci da hare-haren da ake kai wa maikatan su yayin gudanar da ayyukan su abin al’ajabi ne.

Ya ce harin ya na kai ga sun ji munanan raunuka da rasa rayukan su da kuma lalacewar makaman su.

A karshe ya ce motocin sintirin da aka kaddamar ga hukumar, sun zo ne daga karkashin gwamnatin tarayya a wani mataki na bas u kwarin gwiwa a kan ayyukan su dan kwarin gwiwar gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.