Home Labaru Ilimi Karin Wa’Adi: Shugaba Buhari Ya Sake Naɗa Shugaban JAMB Da Na N.U.C

Karin Wa’Adi: Shugaba Buhari Ya Sake Naɗa Shugaban JAMB Da Na N.U.C

70
0
Gargadi: Shugaba Buhari Ya Yi Magana A Kan Rikicin Shugabancin APC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar da sake naɗin shugaban JAMB Farfesa Ishaq Olanrewaju Oloyede da Shugaban hukumar Jami’o’i Farfesa Abubakar Adamu Rasheed.

Hakan na kunshe ne cikin watan sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar ilimi Ben Bem Goong ya fitar.

Wannan ya biyo bayan shawarar da ministan Ilimi Adamu Adamu ya bayar ne.

An nada su ne duk na tsawon shekaru biyar, wanda hakan ya fara aiki daga 1 ga watan Agusta 2021.

Haka kuma ya sake naɗa Dr Hamid Bobboyi shugaban hukumar ilimin bai daya a karo na biyu na tsawon shekaru hudu masu zuwa shima zai fara aiki a ranar 1 ga watan.