Home Labaru Kiwon Lafiya Karin Mutum 2 Sun Kamu Da Coronavirus A Najeriya

Karin Mutum 2 Sun Kamu Da Coronavirus A Najeriya

143
0
Mutum 2 da aka kara gano suna da cutar sun dawo ne daga kasashen waje, inji WHO.
Zuwa yanzu jihar Legas ce kan gaba da mutum 30 masu cutar a jihar.

An gano karin  wasu mutum biyu da suka kamu da cutar coronavirus wadda aka samu bullarta a jiha biyar a fadin Najeriya.

Da hakan ne adadin wadanda suka kamu cutar ya karu zuwa 42 a kasar, a cewar Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka (NCDC),  a ranar Talata. 

Hukumar ta bayyana cewa an samu karin masu dauke da coronavirus ne a jihohin Legas da Ogun.

Ta kara da cewa zuwa yanzu cutar ta bazu a Jihohin Legas, Ogun, Oyo, Ekiti, Edo da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.

Mutum 29 ne suka kamu da cutar a jihar Legas sai kuma mutum 7 a Abuja. Akwai kuma mutum 3 a Ekiti; 1 a Oyo da wani 1 a jihar