Home Labarai Karin Haske: An Bayyana Dalilin Da Ya Sa Tinubu Ya Sallami Ministocin...

Karin Haske: An Bayyana Dalilin Da Ya Sa Tinubu Ya Sallami Ministocin Sa

55
0
download (23)
download (23)

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa sallamar ministoci da shugaban nasa ya yi ya dogara ne ga irin kallon da yadda ƴan Najeriya ke yi wa ministocin.

A wata hira da manema labarai, Onanuga ya ce Tinubu ya yi amfani da tunanin ƴan Najeriya ne.

Ya ce A lokacin da aka rantsar da ministocin, shugaban kasa lallai ya shaida cewa yana da ƙarfin ikon ɗauka da sallamar mutum aiki kuma ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ya kori duk wani ministan da ya fahimci ba ya aikin da ya kamata.

Onanuga ya ƙara da cewa sallamar ministocin ba lallai na nufin cewa ba su yi abin da shugaba Tinubun yake tsammani daga gare su ba.

Leave a Reply