Home Labaru Karin Farashi: Kungiyar Kwadago NLC Za Ta Yi Taro Kan Janye Tallafin...

Karin Farashi: Kungiyar Kwadago NLC Za Ta Yi Taro Kan Janye Tallafin Mai

85
0

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta yi wani taro na manyan shugabannin ta domin daukar matakin da ya kamata bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cire tallafin mai, abin da ya sa farashin ya tashi da kusan ninki uku.

Sakataren kungiyar Nasir Kabir ya sheda cewa shugabannnin sun yi wannan ganawa ne ta na’urar intanet ta Zoom.

Tun bayan furucin da Shugaba Tinubu ya yi ne kasa ta fada wani yanayi na tashin farashin man da kuma dogayen layin ababan hawa a gidajen sayar da mai.

Kafin yanzu dai ana sayar da man ne a farashin da ya kama daga naira 180 zuwa 220 kan kowa ce lita, a sassan kasa daban-daban.

Tun da aka shiga wannan yanayi ne kungiyar kwadagon ta sha alwashin yin fito na fito da gwamnati a kan batun janye tallafin man, ta ce ba za ta amince ba, saboda cire tallafin zai jefa al’umma a cikin wahala.

Leave a Reply