Home Labarai Kare Rayuka: Sojoji Sun Kashe Dan Bindiga Sun Ceto Mutum 15 A...

Kare Rayuka: Sojoji Sun Kashe Dan Bindiga Sun Ceto Mutum 15 A Zamfar

58
0

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta ‘Operation Hadarin Daji’ sun kashe wani dan bindiga tare da ceto mutum 15 da aka sace a Jihar Zamfara.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Sulaiman Omale ya fitar a Gusau a ranar Talata.

Ya ce a wani artabu da aka yi, dakarun Operation Hadarin Daji sun hallaka wani gagarumin dan bindiga a yankin Tsohuwar Tasha da ke Karamar Hukumar Kauran Namoda a Jihar Zamfara.

Omale ya ce, a yayin artabun, maharan sun gudu, sojoji kuma sun kashe daya daga cikin maharan a hanyar su ta tserewa zuwa daji.

A cewar sa, wadanda aka sace sun hada da mata takwas da maza bakwai.

Leave a Reply