Home Home Kare Muhalli: Kenya Za Ta Binciki Yadda Aka Sace Mata Bishiyoyin Kuka

Kare Muhalli: Kenya Za Ta Binciki Yadda Aka Sace Mata Bishiyoyin Kuka

41
0

Shugaban Kenya William Ruto ya umarci ma’aikatar muhalli da kula da gandun dazuka ta gudanar da bincike kan batun tumɓuke bishiyoyin kuka ana fita da su zuwa ƙetare.

Matakin ya zo ne bayan rahotanni kan damuwar da masu rajin kare muhalli ke nunawa, game da safarar manya-manyan bishiyoyin daga ƙauyukan Kilifi zuwa ƙasar Georgia.

A cikin makon jiya ne wata jarida ta ba da rahoton cewa Hukumomin Kenya sun ba da izini ga wani kamfanin ƙetare, na ya cire bashiyoyin don amfanin bunƙasa dandalin tsirrai tsawon shekara biyu.