Kare Kai: An Yi Dauki Ba Dadi Tsakanin ‘Yan Sa Kai Da Masu Satar Mutane
Da alama matsalar tsaro a Najeriya ta fara kai talakawa bango matuka saboda sun fara yin gangami suna shiga dazuka don farautar masu satar shanu da mutane suna garkuwa da su don neman kudin fansa.
Jama’a daga yankunan kananan hukumomin da ke makwabtaka da dajin Kamako ne suka yi wani gangamin sa kai inda suka hadu a gari Dungun Ma’azu da ke yankin karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina suka shiga dajin domin kai wa maharan da ke addabar yankunan su samame.
Wani ganau ya shaida wa BBC cewa, mutane akalla sama da 500 daga jihohin Katsina da Kaduna suka yi wannan gangami inda suka shiga wannan dajin.
Ganaun wanda bai bayyana sunan sa ba, ya ce an yi karan batta sosai tsakanin ‘yan sa kan da kuma masu satar mutane.
Ya ce an kashe masu satar mutane akalla 40, yayin da aka kashe ‘yan sa kan da suka shiga cikin dajin 21.
Ya ce, samamen da mutanen garuruwan suka kai wa masu satar mutanen, ya yi matukar tasiri, saboda ko da aka koma washegari ba a samu kowa ba duk sun gudu.
Ganaun ya ce Jama’a sun ga hukumomi ba su dauki wani mataki ba a kan irin koken da suke kai musu na satar mutane domin kudin fansa da kuma hare-haren da ake kai wa cikin kauyuka ana kashe mutane ba bu gaira ba bu dalili, wannan shi ya sa mutane suka dauki wannan mataki.