Babban limamin Cocin Katolika ta Sakkwato Matthew Hassan
Kukah ya soki lamirin tsarin da ake bi wajen raba tallafin rage
raɗaɗi ga ‘yan Najeriya, ana tsakiyar fama da mawuyacin
tsananin rayuwa a ƙasar.
Gwamnatoci a dukkan matakai sun ɓullo da hanyoyin bayar da tallafin rage raɗaɗi, bayan cire tallafin man fetur.
Sai dai, da yake jawabi game da batun tsarin raba tallafin rage raɗaɗi, Bishop Kukah ya ce akasarin mutane ba sa samu. Ya nuna cewar a lokuta masu yawa kaso mai yawa na irin wannan kuɗi, sace su ake yi.
Malamin addinin Kiristan na wannan bayani ne lokacin da yake zantawa da gidan talbijin na Channels, inda ya kara da cewa Al’ummar Najeriya na buƙatar suga ga wani ƙwaƙƙwaran shiri da gwamnati za ta ɓullo da shi, wanda zai taimaka wajen raba mu da irin wannan bin layi muna karɓar tallafi duk da ba a yaƙi muke yi ba.
Ya kara da cewa tsagwaron zubar da mutunci ne a ga ‘yan Najeriya suna bin layi kullum a cikin rana, suna jiran su karɓi buhun shinkafa, wadda mai yiwuwa ba za ta samu ba, ba kuma don ba a bayar da kuɗin ba, amma sai don sanin cewa duk wanda ya ba da kuɗi a Najeriya daga gwamnatin tarayya yana da masaniyar cewa, wani ƙwaƙƙwaran kaso na kuɗin, a ko da yaushe sacewa ake yi.