Home Ilimi Karatun Sakandare:  Sabon Tsari Zai Fito A Watan Satumba

Karatun Sakandare:  Sabon Tsari Zai Fito A Watan Satumba

80
0
Tahir Mamman
Tahir Mamman

Gwamnatin Tarayya na shirin gabatar da sabon tsarin karatu ga dukkanin makarantun sakandare a fadin kasa a watan Satumban 2024.

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne, ya sanar da hakan ga hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare (JAMB).

 Ministan y ace ana aiki tukuru don tabbatar da cewa an gabatar da sabon tsarin karatu na makarantun sakandare a watan Satumba/

Ya yi nuni da cewa, an fara aikin ne a shekarar da ta gabata kuma za a gudanar da taron masu ruwa da tsaki a ranar 6 ga watan Agusta, 2024 kan sabon tsarin karatun.

A baya-bayan nan, Hukumar Ilimin Sakandare ta Kasa, ta yi Allah wadai da halin da manyan makarantun sakandaren ke ciki,

tare da yin kira a hada kai don shawo kan wasu kalubalen da ke tattare da ilimi a kasa.

Hukumar ta lissafa wasu kalubale da fannin ilimi ke fuskanta, da suka hada da karancin kayan koyarwa, nagartattun malamai, tsofaffin manhajoji, dakunan karatu da dakunan gwaje-gwaje.

Leave a Reply