Home Labaru Karatun Bogi: Kotun Daukaka Kara Ta Fatattaki Dan Majalisar APC

Karatun Bogi: Kotun Daukaka Kara Ta Fatattaki Dan Majalisar APC

895
0
Garba Muhammad Gololo, Dan Majalisar Jam’iyyar APC
Garba Muhammad Gololo, Dan Majalisar Jam’iyyar APC

Kotun daukaka kara da ke zama a birnin Jos na jihar Filato, ta kwace kujerar dan majalisar jam’iyyar APC Garba Muhammad Gololo, bayan ta kama shi da laifin amfani da takardun karatu na bogi.

Alkalin kotun mai sharia E.Igor ya yanke hukuncin, inda ya fatattaki Gololo daga majalisar wakilai a matsayin mai wakiltar mazabar Gamawa ta jihar Bauchi.

Alkalin ya ce, kotun ta kama Gololo ne da laifin amfani da shaidar karatun digiri ta bogi, kuma hatta shaidar kammala bautar kasa ta NYSC da ya bayyana wa hukumar zabe ta bogi ce.

Wani dan jam’iyyar NNPP Isa Muhammadu Wabu ne ya kalubalanci nasarar da Gololo ya samu a zaben shekara ta 2019, inda ya zargi Gololo da amfani da takardun karatun da ya ke ikirarin ya yi a jami’ar jihar Legas.

A karshe Alkalin ya ba hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC umarnin ta gudanar da sabon zabe a cikin kwanaki 90 masu zuwa.

Leave a Reply